Wednesday, 24 January 2018

Dangote zai iya fidda mutum miliyan 2 daga talauci

Kudin ruwan da attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka Aliko Dangote yake samu zai iya fidda kimanin mutum miliyan biyu daga talauci, a cewar kungiyar Oxfam. Kungiyar ba da agajin ta ce ta tazarar da ke tsakanin talaka da attajiri ta karu a bana.

Kamar yadda kungiyar wadda take a Birtaniya ta ce mutum 42 biloninoyi sun samu dala biliyan 3.6 a duniya.

Hakazalika kungiyar ta ce kashi daya cikin 100 na attajiran duniya ne suke tafiyar kaso 82 cikin 100 na dukiyar da ke fadin duniya.

Oxfam ta ce abin da ya kara taimakawa manyan attajiran wajen tara dimbin dukiyar shi ne yadda wadansu daga cikinsu suke kauce wa biyan haraji.

Har ila yau akwai kuma batun yadda suke amfani da gwamnatoci wajen yin dokoki da za su ci gajiyarsu, a cewar kungiyar.

Sai dai masana a fannin hada-hadar kudi sun sanya alamar tambaya game da wadansu daga cikin abubuwan da kungiyar take ikirari.

Manyan attajirai shida da suka fi kudi a duniya

1. Jeff Bezos $ Biliyan 110.7 (Ba'amurka)
2. Warren Buffett $Biliyan 92.6 (Ba'amurka)
3. Bill Gates $Biliyan 92.6 (Ba'amurka)
4. Amancio Ortega $Biliyan76.4 (Dan Spain)
5. Mark Zuckerberg $Biliyan 74.7 (Ba'amurka)
6. Carlos Slim Helu $Biliyan 69.8 (Dan Mexico)

Shugaban kungiyar Oxfam Mark Goldring wannan rahoton ba labari ne mai dadi ba ga duniya.

Rahoton yana zuwa ne a daidai lokacin da aka fara wani babban taro tattalin arziki na duniya a birnin Davos na kasar Switzerland.

Manyan 'yan kasuwa suna halartar taron ne duk shekara don tattauna hanyoyin da za su yi amfani da dukiyarsu wajen taimakon sauran mutane mabukata.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment