Tuesday, 9 January 2018

Dusar kankara ta zuba a Saharar kasar Aljeriya saboda tsananin sanyi

Wani abin mamaki da birgewa daya faru a kasar Aljeriya shine, dusar kankara ta zuba akan yashin/rairan Sahara ranar Lahadin data gabata saboda tsananin sanyi, wannan dai shine karo na uku da dusar kankarar ke zuba a cikin Sahara cikin shekaru Arba'in da suka gabata.Dusar kankarar ta zuba a shekarun 2016 da 2017 da suka gabata.

Kankarar sanyin ta zubane a birnin Ain Safra na kasar ta Aljeriya kamar yanda Dailymail ta ruwaito.

Wani me daukar hoto ya bayyana cewa sun tashi ranar Lahadi da safe kawai sai sukaga dusar kankara ta mamaye ko'ina, yace, sai da misalin karfe biyar na yamma sannan dusar kankarar ta fara narkewa saidai sahun kafafuwa.
A shekarar 2016 ne wani birni na kasar ta Aljeriya aka ga dusar kankarar a watan Disamba, sannan kuma an sake ganin dusar kankarar a birnindai a watan janairu na shekarar 2017. Rabon da aga dusar kankarar a kasar Aljeriya tun shekarar 1979.


No comments:

Post a Comment