Saturday, 13 January 2018

El-Zakzaky ya gana da manema labarai

Shugaban kungiyar 'yan Uwa Muslumi da aka fi sani da 'yan Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya gana da manema labarai karon farko tun bayan da aka kama shi. Rundunar sojin kasa ta Najeriya ce ta kama Sheikh El-Zakzaky a watan Disambar shekarar 2015 a Zaria da ke jihar Kaduna, bayan sojoji sun yi wa gidansa kawanya.


Wata sanarwa da kafar watsa labarai ta PR Nigeria na dauke da da hotunan Malamin a lokacin da yake jawabi ga 'yan jarida.

Gidan talbijin na Channels ya ambato Sheikh El-Zakzaky na cewa yana nan a raye kuma lafiyarsa lau.

Ya kuma gode wa 'yan Najeriya saboda addu'o'in da suke yi masa.
A makon nan ne dai aka yi jitar-jitar cewa Malamin ya rasu.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment