Monday, 22 January 2018

Fadakarwa me amfani akan yin amfani da yanar gizo>>Daga Sheikh Isah Ali pantami

Fasahar yanar gizo tazo da ci gaba me dimbin yawa wanda ya kawowa rayuwar dan Adam sauki sosai, mafi yawancin mutane a wannan zamani suna amfani da yanar gizo ta hanyoyi daban-daban da suka da sada zumunci, aika sakonni, karanta labarai, gudanar da ayyuka daban-daban, karatu, sana'o'i dadai sauransu, saidai kuma wajan amfani da yanar gizo sai mutum yabi a hankali domin akwai abubuwa da dama da zasu iya dauke mai hankali har ya shiga wata irin rayuwa ta daban.


Irin wannan ne yasa, daya daga cikin Shehunan malamanmu, Sheikh Isa Ali Pantami yayi wani jan hankali me matukar amfani akan yanda mutum ya kamata yayi amfani da yanar gizo dan ya tsira Duniya da Lahira.

Malan yayi amfani da dandalinshi na sada zumunta da muhawara na shafin Twitter dan yin wannan jan Hankali kamar haka:

 "Tunatarwa: a koda yaushe kayi tunani kamin ka saka wani sako a yanar gizo. Duniya tana bukatar masu karfafa hadin kai da kyakyawar halayya da zaman lafiya ba ta bukatar masu karfafa shedanci, rashin zaman lafiya, kiyayya ko rudani ba. ka tuna cewa labaran kalaman da ka rubuta a yanar gizo, zasu kasance ko da bayan baka(ka mutu) kuma zasu jawo maka yabo ko kuma Allah wadai yayin da baka nan. Kayi tunani". 

"Ka tuna da cewa, hannayenka zasu karanta dukkan abubuwan daka rubuta a yanar gizo, ranar tashin Al-Qiyama a gaban mahaliccinka, wanda ya Qagi Duniya. Ka rubuta abu me kyau wanda yake kan hanyar daidai, saboda ka samu karantashi  cikin sauki da kwaciyar Hankali ranar tashin Qiyama."
"Ka tuna da cewa, Mala'iku suna nan kanka suna karanta duka binda kake rubutawa a yanar gizo, 
kuma suna rubuta maka lada ko zunubi, daidai da irin abinda ka rubuta. Ku sani har abubuwan da muke yi a yanar gizo Mala'iku na rubutawa. ka rubuta abu me kyau kuma ka tabbatar da ingancin labari(kamin ka rubutashi)."

Addini ya karantar damu taimakon 'yan uwanmu wajan ayyuka na gari da kyakyawar Halayya da kuma tsoron Allah. Haka kuma an umarcemu da kada mu taimakawa junanmu wajan yin sabo da kiyayya. A koda yaushe mu rika kokarin yada abu me kyau mu kuma kiyaye yada shedanci da kiyayya. Zamu ga sakamakon duk abin da mukayi a ranar tashin kiyama. Mu hankalta."
"Shekarau hamsin da zasu zo nan gaba ko ma fiye da haka, 'ya'yanka, da jikokin ka da danginsu, zasu iya kacibis da abinda ka rubuta a yanar gizo su kuma karanta a matsayin ka na magabacinsu. Wane irin abun kake bari da zasu tunaka dashi a yanar gizo? Sirikinka ma zai iya kicibis da abinda ka rubuta a yanar gizo ya karanta".
"Kana tunawa kanka cewa a ranar tashin Qiyama za'a tambayemu akan duk wani abu da muka rubuta a yanar gizo? ka koma ka duba irin abubuwan daka rubuta a yanar gizo, kawa kanka Hisabi kamin a maka Hisabin gaskiya".
"Yan uwana Maza da Mata ku misalta cewa yau gaku a gaban Allah ranar tashin Qiyama. Sai Allah ya ce muku "Ka karanta littafinka(da suka hada da abubuwan da kuka rubuta a shafukan yanar gizo, Twitter, Facebook, Whatsapp, Instagram da saurannsu) kai da kanka ka isa yiwa kanka Hisabi a wannan rana".
"Ranar Qiyama tabbas ce, zata zo, babu kokwantao, saboda haka ina shawartarku da ku duba dukkan wani abu da kuka rubuta a yanar gizo. Duk wani me cutarwa ko na shedanci ya kamata a gogeshi sanan a tuba. Idan ba hakaba zai jawo fushin Allah da zai iya mutum zuwa wuta. Ayi tunani".
"Idan kana cikin fushi, kada ka rubuta komi a yanar gizo, yawancin maganganun da akayi su cikin fushi, anayin dana saninsu daga baya, kuma sukan sa wanda aka zalunta ya juya ya koma me yin zaluncin shima. An umarcemu damu fadi Alheri ko muyi shiru. Shiru ma maganace".

No comments:

Post a Comment