Sunday, 14 January 2018

Fati Nijar tayi kira da a taimakawa 'yan gudun hijira: Wani ya kunduma mata zagi

Da alama tauraruwar mawakiyar Hausa, Fati Nijar ta kaiwa wasu 'yan gudun Hiira ziyara sansaninsu, a wasu hotuna data saka a dandalinta na sada zumunta da muhawara, Fatin tayi kira da cewa a taimakawa mutanennan.To saidai da alama wani beji dadin wannan magana da tayi ba, domin kuwa kunduma mata zagi yayi ina yace "saidai a taimakawa Uwarki. Muna fuka".

Ashe dama umarni da kyakkyawan aiki yana zama aibu?

No comments:

Post a Comment