Wednesday, 17 January 2018

"Gurbatattun malamai mukeso mu sallama dan daukar kwararru">>Gwamna El-Rufai na Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yayi suna sosai tsakanin Gwamnonin Najeriya, musamman saboda maganar sallamar malaman makaranta da yayi a jihar ta Kaduna, a kokarin da yake na kawo gyara a harkar ilimin jihar.


Wasu sun yaba, yayinda waau sukayi Allah wadai da tsarin na Gwamnan, amma shidai ya tsaya kai da fata yana kare wannan kudiri nashi.

A wani sako daya fitar gwamnan yace:

"Ba kowa da kowa muke so mu sallama aiki ba. Muna son mu sallami gurbatattatun malamai ne don mu dauki kwararru. Wannan dalilin ya sa za mu dauki sababbin malamai 25,000 don maye gurbin 21,780 da muka sallama."

No comments:

Post a Comment