Thursday, 25 January 2018

Gwamnatin jihar Kaduna ta fara yin gwajin sabbin malaman da zata dauka aiki

A kokarin da take na kawo cigaba me amfani a fannin Ilimi, Jihar Kaduna ta fara yin gwaji da tantance sabbin malaman makaranta da zata dauka aiki a jiya Laraba, a wata sanarwa da gwamnan ya fitar ya bayyana yanda gwajin ke gudana.
Gwajin malaman makarantar firamare da Gwamnatin Jihar Kaduna za ta dauka ya kankama yau Laraba 24/01/2018 sosai kuma yana tafiya cikin nasara. Ana dai gwajin malaman ne ta hanyar ganawa da su ido da ido inda ake yi musu tambayoyi kan darussan da suka karanta, da sanya su karatu da rubutu,  da yin magana da harshen Ingilishi da sauransu da kuma tantance takardun makarantarsu.

Kwamitin da aka kafa da suke wannan aikin sun hada da kwararru kuma amintattun tsoffafin ma'aikata da suka ajiye aiki da kuma wadanda da suke aiki,  har da kungiyoyi daban daban da suka hada da wakilan TRC da sauransu. 

Za a kuma ci gaba da wannan gwaji har na tsawon kwana uku, don wadanda ba su samu sun yi yau ba, suna iya yi gobe ko jibi. 

Allah ya ba da sa'a ya kuma sa talakawan Jihar Kaduna su amfana da kokarin da muke yi na farfado da ilimi a jihar.

No comments:

Post a Comment