Monday, 8 January 2018

Gwamnatin jihar Kaduna tasha alwashin korar duk ma'aikacin daya tafi yajin aiki

Gwamnan jihar Kaduna, malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya gargadi malaman makarantar Firaimare na jihar akan yajin aikin da suke shirin farawa ayau da cewa yasa a bude rigista ta musamman a dukkan makarantun firaimare na jihar domin daukar sunayen malaman da sukazo aiki da wadanda basu zoba, ya kara da cewa duk malamin daya sake yaki zuwa aiki da sunan yajin aiki to za'a dauki mayakin daya dace akanshi wanda zai ida rasa aikinshi.Gwamnan yace yajin aikin baya bisa kan ka'ida saboda haka gwamnati bazata lamunci hakan ba.

Malaman firaimare na jihar Kaduna dai zasuje yajin aikinne saboda nuna rashin amincewa da korar sama da malamai dubu ashirin da gwamnatin jihar tayi dalilin faduwa jarabawar tantancewa da aka musu.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya dage cewa yanayin hakanne dan inganta karatun firaimare a jihar inda yace 'ya'yan talakawane a makarantun kuma hakkin basu ingantaccen ilimi yana wuyan gwamnati, ya kara da cewa bashine ya fara korar malaman makarantar firaimarenba, koda marigayi gwamna Yakowa ya kori wasu malamai da basu cancantaba kuma ya baiwa wadanda ke ciki damar shekaru biyar dansu je su karo ilimi amma kwalliya bata biya kudin sabuluba.

No comments:

Post a Comment