Tuesday, 23 January 2018

Gwamnatin jihar Kaduna zata ginawa malaman da za'a tura kauyuka gidaje: Jihar ta fara samun tallafin Ilimi daga kasashen Duniya

A kokarin da yake na kawo ci gaba a harkar Ilimi a jihar Kaduna, Gwamna Malam Nasiru El-Rufai yace ya lura da yawan malaman makaranta ifan aka kaisu kauye koyarwa basu son zuwa saboda rashin kyawun gurin zama, saboda haka gwamnan yayi tsari na musamman da za'a ginawa malamai gidajen zama a kauyukan jihar.Gwamnan yace yanzu haka ana kan tsara yanda za'a fara gina gidajen malaman a kauyuka, yace, shugabannin makarantun za'a gina  musu gidaje masu dakuna uku-uku, su kuma malamai za'a gina musu gidaje masu dakuna biyu-biyu.

Haka kuma a wata sanarwa ta daban, gwamnan ya bayyana cewa duk da yake wasu na sukar tsarin da gwamnatinshi ta kawo akan gyaran Ilimi amma wasu kasashen Duniya da kungiyoyin agaji na kasa da kasa suna bibiyar yanda yake kokarin habbaka harkar ilimin jihar kuma tuni har ya fara samun tallafi daga irin wadannan kungiyoyi da kasashe.No comments:

Post a Comment