Sunday, 7 January 2018

Gwamnatin tarayya ta samar da ayyukan yi guda miliyan takwas>>Ministan Gwadago

Ministan kwadago da Ayyuka Chris Ngige ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samar da ayyukan yi guda miliyan takwas a cikin kasa da shekaru uku da tayi tana mulkin Najeriya.Ministan ya bayyana hakane ga 'yan jaridu a jihar Anambra ranar Juma'ar data gabata, a gurin bude wata cibiyar koyar da sana'o'in hannu, ya kara da cewa ayyukan da gwamnatin ta samar ayyukane na dogaro dakai, wanda mutum zai iyayi da hannunshi, da suka hada da noma, aikin kafinta, da aikin birkila, dadai sauransu, yace gwamnatin ta yanke shawarar samar da irin wadannan ayyukane saboda aikin ofis yana wuyar samu yanzu, duk wanda yace zai jira aikin ofis to zai dade bai samu aiki ba.

Ya bayar da misali, inda yace a babban birnin tarayya, irin masu sana'o'in hannu suna samun kudi sosai, yawanci dubu goma suke amsa idan sunyi aiki, misali ace sun samu aiki sau biyar a wata, irin kudin da za'a biyasu, masu aikin ofis nawa ke karbar albashin daya kai haka?

Ya kara da cewa yawancin yanzu sana'o'in hannu sunfi aikin ofis samar da kudi.

No comments:

Post a Comment