Tuesday, 30 January 2018

"Hana Ni Zuwa Kano Zalunci Ne">>Inji Sanata Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce gwamnatin Kano da 'yan sanda da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar nan ne suka hada baki suka hana shi zuwa Kano.


Sanatan, wanda tuni dubban masoyansa daga sassa daban-daban na kasar nan suka halarci jihar Kano domin tarbar sa a yau Talata, ya kara da cewa abin mamaki ne a matsayinsa na Sanata a ce an hana shi zuwa mahaifarsa don ya gana da iyayensa, 'yan uwansa da masoyansa.

Ya kuma kara da cewa bai kamata a ce ana amfani da jami'an tsaro a harkar siyasa ba.
Rariya.

No comments:

Post a Comment