Saturday, 20 January 2018

Har daga kasashen waje anzo kallon fim din Gwaska ya Dawo na Adam A. Zango


Koda gani babu tambaya, idanuwan ku sun nuna maku kalilan daga cikin cinciridon mutanen da su ka yo tattaki don ba idawan su abinci game da nuna Gwaska ya Dawo da aka fara a yau. Ko shakka babu Gwaska ya yi kira kuma mutan Kano sun amsa, don kuwa a ranar farko an samu dimbin makallata wadanda aka dade ba a tara su a sinimar ba. Har sai dai ta kai an yi kutsotsoniya gami da turereniya ya yin shiga kallon fim din.


Masoya daga mabambanta jihohin arewa ne suka halarci haska fim din. Hatta mutanen Kasar Ghana sunzo dan kashe kwarkwatar idanuwan su.Hakika bukatar maje haji sallah, kuma ko da ganin ruwan damina ka san ba na noman rani ba ne. An daka an raya yanzu aka gane na moriya wato gwaska.

Fim din ya tsaru. Kuma ya shiryu, sannan an samu kyawun sauti rangadadau.Kowa yana ala sanbarka.
Kannywood exclusive.

No comments:

Post a Comment