Sunday, 7 January 2018

Hoton hannun Adam A. Zango sanye da zobe me sunan Allah da Annabi ya jawo cece-kuce

Wannan hannun tauraron fina-finan Hausa kuma mawakine, Adam A. Zango dake dauke da wani zobe da aka rubuta sunan Allah da Annabi(S.A.W), jarumin ya saka wannan hotonne a dandalinshi na sada zumunta da muhawara, kuma ya dauki hankulan mutane sosai.Wasu dai sun yaba, haka wasu sun kushe yin hakan da Adamu yayi.

Wasu sunce saka irin wannan zoben yana bukatar taka tsantsan, domin kada mutum ya shiga inda be kamata dashiba, yayinda wasu ke ganin cewa saka hotonma kwata-kwata beda ma'ana.

Adamu dai yaje jihar Legas ne inda ya halarci gurin Maulidi da akayi a daren jiya, kuma bayan da jama'a suka ganshi a gurin sun yita shewar murna da jin dadi.

No comments:

Post a Comment