Friday, 5 January 2018

"Ina godiya ga 'yan Najeriya bisa addu'o'in da sukewa dana, Yusuf">>A'isha Buhari

Uwargidan shugaban kasa,Hajiya A'isha Buhari ta mika godiyarta ga 'yan Najeriya bisa irin addu'o'in da sukewa dan nata, Yusuf Buhari har Allah yasa ya fara warwarewa daga jiyyar da yakeyi a gadon Asibiti sanadiyyar hadarin babur da yayi.


/>
Hajiya A'isha Buhari a cikin wani sako data saki ta kuma godewa likitoci da suka bayar da gudummuwa sosai wajan ganin dan nata, Yusuf ya fara murmurewa kuma tace ta gode, Allah ya sakawa kowa da Alheri.


No comments:

Post a Comment