Monday, 29 January 2018

"Ina son musulmai suma suna sona">>Shugaban Amurka Donald Trump

A wata hira da yayi da manema labarai, Shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump ya bayyana cewa shi yana son dukkan mutane, saidai kawai idan mutum shi ba na gari bane to dolene suyi abinda ya kamata a kanshi. Ya kara da cewa tun lokacin da yake yakin neman zama shugaban kasa musulmai suna sonshi kuma yasan har yanzu ma suna sonshi.Trump dai ya fito da tsare-tsare na hana wasu kasashen musulmai shiga kasar ta Amurka tun bayan daya zama shugaban kasa, haka kuma kwanannan ya yada wata magana da wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayi kan addinin musulunci na kasar Ingila inda aka zargeshi da nuna goyon bayan wannan kungiya.

Saidai ya bayyana cewa ba'a fahimceshi bane akan wancan magana daya yada.
Metro UK.

No comments:

Post a Comment