Monday, 29 January 2018

Inya murar data musulunta, A'ishat Obi ta musuluntar da 'yan uwanta biyu

Baiwar Allahn nan Inyamura da labarin musuluntarta ya watsu sosai a shafukan sada zumunta da muhawara me suna A'ishat Obi, wadda dallilin kyawawan halayyar kawarta musulma yasa ta amshi addinin musulunci, itama ta jawo 'yan uwanta biyu, Namiji da tamace wanda tace 'yan uwane na jini a gareta suma sun anshi addinin musulunci.A'isha ta bayyana hakane a dandalinta na sada zumunta da muhawara inda tace, Chijoke Obi da Chiamaka Obi yan uwana na jini daga jihar Imo sun amshi addinin musulunci a yau, tace sun canja sunayen su zuwa Rahaman Obi ita kuma macen Rashidat Obi.

Gaskiya A'isha tana wa addinin Allah aiki, domin idan za'a iya tunawa kwanakin baya, bayan ta karbi musulunci ta rika kira ga 'yan uwanta da suka karbi addinin musulunci dasu tashi su nemi ilimi haka kuma tayi kira ga wadanda suke so su amshi addinin dasu fito fili su amsa kar su ji tsoron kowa.

Allah ya saka mata da Alheri ya kuma karo mana irinsu

No comments:

Post a Comment