Monday, 22 January 2018

Inyamurai sun amince shugaba Buhari ya sake tsayawa takara a shekarar 2019

A ganawar da sukayi da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, 'yan Jam'iyyar APC na yankin Inyamurai sun bayyanamai cewa shine zabinsu a zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu, jaridar Punch ta ruwaito cewa duk da yake ganawar da sukayi da shugaban kasar a sirrance aka yita amma shugaban tafiyar, ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu ya bayyanawa manema labarai abinda suka tattauna a taron.


Yace sun gayawa shugaba Buharine irin shawarar da suka yanke a wani zama da sukayi tun watan Disambar shekarar 2017 data gabata inda suka amince da tsayar dashi a matsayin dan takararsu na shugaban kasa a zaben 2019 idan Allah ya kaimu.

Onu ya kara da cewa shugaban kasar yaji dadin wannan ziyara da suka kaimishi, musamman saboda irin manyan mutanen da suke tare dasu a wannan tafiya, domin akwai tsaffin gwamnoni da 'yan majalisa na tarayya da sauran tsaffin ma'aikatan gwamnati.

No comments:

Post a Comment