Wednesday, 24 January 2018

Jigo a jam'iyyar kin jinin addinin musulunci ya musulunta a kasar Jamus

A Photo of AfD party board member Arthur Wagner. (Sources: AfD Hovelland)
Allah me shirya wanda yaso, daya daga cikin jigon 'yan jam'iyyar kin jinin baki da musulmai a kasar Jamus watau AFD a takaice me suna Arthur Wagner ya musulunta, Jam'iyyar dai ta masu tsatstsauran ra'ayice akan baki da musulmai a kasar ta Jamus.


Kuma har ta samu shiga majalisar kasar ta Jamus saboda wani tsari data fito dashi na kin jinin musulunci da tsaurara dokokin shiga kasar ta Jamus dan maganin 'yan cirani da 'yan gudun hijira masu zuwa kasar sun ragu.

Jam'iyyar ta tabbatar da komawar Arthur Wagner Musulunci kuma tace ba wani abin damuwa bane a gareta domin dama a cikin jam'iyyar tasu akwai wakilan adinin musulunci da Kiristanci haddama 'yan Luwadi.
DailySabah

No comments:

Post a Comment