Friday, 26 January 2018

Jirgi ya kade wani mai daukar hoton 'selfie'

Dubban Indiyawa ne, suka kalli hoton bidiyon wani mutum da jirgin kasa ya kade shi a lokacin da ya ke daukar hoton selfie. Wannan lamari dai ya faru ne a Hyderabad, bayan da mutumin mai suna T Siva, ya yi watsi da gargadin da wani mutum da ke kusa da layin dogon ya yi masa da kuma hon din jirgin, a lokacin da ya ke daukar hoton na selfie.


Mr Siva, bai mutu ba, amma kuma ya samu raunuka a kansa, inji 'yan sandan da ke aiki a tashar jirgin. Yanzu haka dai ya samu sauki, har ma ya bayyana gaban kotu inda kuma aka ci shi tarar dala kusan takwas, saboda dokar da ya taka ta hana daukar hoton selfie a wuraren da aka hana.

Daukar hotuna a lokutan da jirgin kasa ke tahowa, ya zamo wani abu na ya yi da ke da matukar hadari a India.

Ko a watan Oktoban da ya gabata, wani jirgin kasa ya bi takan wasu matasa uku a lokacin da suke kokarin daukar hoton selfie a jihar Karnataka, yayin da wasu matasan biyu ma a Delhi, suka mutu a irin wannan yanayi.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment