Sunday, 21 January 2018

Kalli Atamfa ta musamman da akayi saboda Kwankwaso

Wasu masoya tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso sun yi atamfa me dauke da tambarin hoto da sunanshi dan nuna soyayya, kamar yanda ake iya gani a wannan hoto.
 Ana dai ta takaddama akan zuwan jagoran siyasar kwankwasiyya jihar ta Kano bayan da ake ga dangantaka tayi tsami tsakaninshi da tsohon mataimakinshi kuma gwamna a yanzu na jihar Kanon, limamin Gandujiyya, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

A ranar 30 ga watannan na Janairune ake saran idan Allah ya kaimu Kwankwason zai kai ziyara jihar ta Kano, Lokaci dai be bar komi ba indai da rai da lafiya.

No comments:

Post a Comment