Friday, 26 January 2018

Kalli hoton barkwanci akan yanda gwamnati ke watsi da lamurran matasa

Wannan wani hoto ne da DW sukayi dake nuna irin yanda gwamnati keyin watsi da harkokin matasa a kasarnan, musamman ta bangaren samar da ayyukan yi, alkaluma dai na kwanakwanannan da hukumar kididdigar ta kasa ta fitar sun nuna cewa an samu karin dubbin mutane da suka rasa ayyukansu.Da yawa matasa na kare karatun jami'a amma su kare babu aikin yi, irin wannan ke kara yawan laifuka a tsakanin al'umma. Allah ya dawo da hankulan shuwagabannin mu su dukufa wajan magance wannan matsala.

No comments:

Post a Comment