Tuesday, 30 January 2018

Kalli hotuna masu daukar hankali na mutumin da yafi kowa tsawo a Duniya da matar da tafi kowace mace Gajarta a Duniya

World's Tallest Man Shortest Woman
Allah me halitta yadda yaso, a nan hotunan mutumin da yafi kowa tsawo a Duniyane me suna Sultan Kosen tare da matar da tafi kowace mace gajarta a Duniya, Jyoti Amge kenan sun hadu a kasar Misra/ Egypt.


Hukumar kula da harkokin al'adu ta kasar Misra din ce ta shirya haduwar wadannan mutane masu daukar hankali dan kayatar da masu yawon bude ido a kasar.

Shi dai Sultan Kosen manomine dan asalin kasar Turkiyya kuma ya shiga kundin tarihin abubuwan bajinta da abubuwan ban mamaki na Duniya a matsayin wanda yafi ko wane namiji dake raye a doron kasa tsawo a Duniya, anyi binciken cewa dalilin girman jikin Sultan shine samuwar halittun dake sa girman jiki fiye da kima a jikinshi.
GettyImages-910721764
Sultan dan shekaru talatin da daya yana cikin mutane goma kacal da Duniyar yanzu ta sani da suka taba kai tsawon sama da kafa takwas a tarihi. Haka kuma Sultan shine ke rike da kambun mutum me hannu mafi girma a Duniya.
 GettyImages-910721752
Ita kuwa Amge wadda itama ta shiga cikin kundin abubuwan ban mamaki da bajinta na Duniya a matsayin mace dake raye a doron kasa mafi gajarta, tana da tsawon kafa biyu da digo daya ne kacal.
'Yar shekaru ashirin da hudu wadda 'yar asalin kasar Indiyace, 'yar fim ce kuma me gabatar da shirye-shiryen gidan talabijin a kasar tata ta Indiya.
MAXIM

No comments:

Post a Comment