Sunday, 21 January 2018

Kalli kauyen da yafi ko'ina sanyi a DuniyaWannan hotunane daga wani kauye dake can yankin Siberia, kusa da kasar Rasha me suna Oymyakon daya dauki hankulan Duniya saboda tsananin Sanyin dake garin, a yanzu dai ana kiyasta cewa wannan gari shine guri mafi tsananin Sanyi a Duniya.Wani dan jaridan daukar hoto daya taba ziyartar kauyen yace, daya fito wace dan yin aikinshi na daukar hoto, sanyi ya rika kada mai kafafunshi kuma yawun bakinshi ya rika zama kankara yana soke mishi harshe, saboda tsananin sanyi.
Kamar yanda ake iya gani a wadannan hotunan, tsananin sanyin yakai har yana daskarar da girar mutane, kuma hakan har ya zamarwa mutanen garin, musamman mata, wani sabon salon kwalliya.
Saboda tsananin sanyi, na'urar dake gwada yanayin garin har bugawa tayi ta daina aiki na dan wani lokaci, saboda abin ya ta'azzara.
Amma duk da wannan tsananin sanyi, mutane na zuwa aiki, a kalla akwai mutane kusan dari biyar dake zaune a wannan gari, kuma har masu yawon bude ido da 'yan jarida na ci gaba da durara zuwa wannan gari.
Saboda tsananin sanyi, masu sana'ar sayar da kifi basa bukatar sakashi a firjin wai dan kada ya lalace, sanyin dake kadawa a garin ya isa ya hana kifin lalacewa.
A shekaru da dama da suka wuce, wannan kauye ba gari bane, wani zangone na makiyaya dake tsayawa suna shayar da dabbobinsu ruwa kamin suci gaba da tafiya, amma daga baya, lokacin yankin yana karkashin tarayyar Sobiyat sai aka mayar dashi gurin zama na din-din-din.

Duk da yake cewa sanyi takurane ga mafi yawan mutane amma a wannan kauye sai ya zama abin birgewa, dan kuwa ko ina ya koma kankara, fari tas, kamar a Fim.


Hatta gashin dabbobi sai an rika karkade musu shi saboda yana daskarewa ya zama kankara.


Boredpanda.

No comments:

Post a Comment