Friday, 5 January 2018

Kalli Masu bin layin mai sun bar motocinsu suna yiwa shugaba Buhari oyoyo a jihar Kaduna

A jiyane shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Kaduna inda ya kaddamar da wasu manyan ayyuka, jama'a da dama sun fito suka tarbi shugaban kasar cikin murna da shewa, sai dai wannan hoton ya fita daban.Domin kuwa kamar yanda kowa ya sani cewa, kusan gaba dayan kasarnan ana fama da matsalar karancin man Fetur inda zakaga motoci sun jera zungureren layi, wasu ma har sai sun kwana akan layin basu samu manba.

Amma sai gashi, shugaba Buhari yazo wucewa ta gefen wani gidan mai inda motoci ke kan layi, mutane basu shareshiba suka juyo, suka bar motocinsu sunata fadin sai baba.

Lallai soyayyar talaka da shugaba Buhari ta musammance.

No comments:

Post a Comment