Monday, 22 January 2018

Kalli sojan da 'yan mata ke wawarshi a Borno

Tun bayan da wani me suna dan Borno ya wallafa hoton wannan sojan da irin yanda yake da farin jini a gun 'yan mata a garin Ngala na jihar Borno, sai labarinshi ya karade shafukan sada zumunta da muhawara, mutane nata fadin albarkacin bakinsu.


Wasu sunyi mamakin irin yanda sojoji da aka saba ganinsu suna mazurai amma ga wani soja zagaye da 'yan mata haka suna ta so su dauki hoto dashi, lallai akwai wani abu na musamman tattare dashi, Dan Borno a cikin labarin daya bayar akan wannan sojan yace duk inda zai wuce gun-gun jama'a, a sansanin 'yan gudun hijirane ko a cikin gari sai kasa 'yan mata nata so su dauki hoto dashi, gashi kyakyawa kuma ya iya mu'a mala.

Saidai wasu na ganin cewa ya kamata yayi hankali da irin 'yan matan dake zuwa kusa dashi domin abokan gaba zasu iya amfani da wannan dama su kaimai hari.

No comments:

Post a Comment