Sunday, 7 January 2018

Kalli yanda wani masoyin kwankwaso ya shirya tarbarshi a ziyarar da zai kai Kano

Wannan hoton wani bawan Allahne da iyalanshi masoyin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa ya shirya tsaf shida iyalanshi dan tarbar Kwankwason a ziyarar da zaikai jihar ta Kano.


Ga abinda ya fada, kamar yanda shafin Rariya suka ruwaito:

'Ni Da Iyalaina Mun Shirya Tsaf Domin Taryar Kwankwaso A Kano'

"Ni da iyalina mun shirya tsaf domin zuwa taryar shugaban kasar mu na gobe a 2019 da izinin Allah, Madugu Uban tafiya, jagoran Darikar Kwankwasiyya na duniya, Injiniya Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso zuwa jiharsa ta haihuwa wato jihar Kano. Kai kuma fa?"

Daga Shafin Sani Lawan Jingau (Garkuwar Kwankwasiyya)

No comments:

Post a Comment