Friday, 5 January 2018

Karanta lokutan da sabbin jiragen kasa zasu rika tashi daga Kaduna zuwa Abuja

A jiyane shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin taragwan jiragen kasa akan titin jirgin kasa na hanyar Kaduna zuwa Abuja, a yau gwamnati jihar Kaduna ta sanar da sabbin lokutan da jirgin zai rika tashi daga Kaduna zuwa Abuja da kuma daga Abuja zuwa kaduna.Ga yanda lokutan suke kamar haka:

Jiragen dai zasu rika sawu hudune a rana.

Da Abuja, jirgin zai rika tashi daga karfe bakwai na safe.

Da kuma tara da minti hamsin.

Sai kuma da yamma, zai rika tashi da karfe biyu da minti ashirin.

Sai kuma karfe shida na yamma zuwa Kaduna.

Daga Kaduna kuma jirgin zai rika tashi zuwa Abuja ne.

Daga karfe shida da mintuna arba'in.

Da kuma goma da mintuna talatin da biyar.

Sai kuma da yamma daga karfe biyu na yamma.

Da kuma karfe shida na yamma.

No comments:

Post a Comment