Monday, 1 January 2018

Karanta sakon sabuwar shekara na Abdulmumini Jibril

Dan majalisar wakilai da aka dakatar me wakilatar mazabar Kiru da Bebeji daga jihar Kano, Abdul mumini Jibril kenan da iyalanshi yake mika sakon taya murnar shiga sabuwar shekarar 2018, a cikin sakon nashi ya kira mutane dasu rike gaskiya domin komi daren dadewa itace zata bayyanaGa sakon nashi kamar haka:


"Barkanmu da sabuwar shekara na bature kowa da kowa, ina  bamu shawarar muyi amfani da wannan lokacin wurin jaddada kauna  da soyayya da kyautatawa iyali da abokanai da jamaa baki daya da jajircewa wurin kyautata dangantakarmu da Allah wurin bauta ma SA da yin kishin kasarmu mai albarka cikin aminci. 


Ya 'Yan  uwa  ina jan hankalin mu da tsayawa akan gaskiya da adalci, tabbas zaka iya  tsintar kanka  cikin JARABAWA MAI DACI DA KUNA, amma a JAJIRCE! Ku sani  kome daren  dadewa GASKIYA ita take tabbata"

No comments:

Post a Comment