Saturday, 13 January 2018

Karanta yanda tattaunawar Zakzaky da 'yan jarida ta kasance ayau

El-Zakzaky
A yaune labari ya samu cewa shugaban kungiyar Shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky ya gana da 'yan jarida karrin farko tun bayan shekaru biyu da sojoji suka kamashi shida me dakinshi Zeenah, wannan bayyana da sheikh Zakzaky yayi bata rasa nasaba da rade-radin da aka rika yi cewa ya mutu a hannun jami'an farin kaya.

Ga dai abinda ya fada a tattaunawar da yayi da 'yan jarida a yau, kamar yanda bbchausa ta ruwaito:

 'Yan jarida: Barka da rana?
'Yan jarida: Ko za ka iya ganawa da mu?
Sheikh El-Zakzaky: Idan sun amince kuma sun ba ni izini (kamar yadda ya ce cikin raha)
Sheikh Zakzaky: Wane hali kake ciki?
'Sheikh Zakzaky: Na samu shanyewar barin jiki a ranar Juma'a 5 ga watan Janairun bana
Sheikh Zakzaky: Jikin ya yi tsanani ranar Litinin, amma daga baya jikin ya yi sauki
'Yan jarida: Yaya kake ji yanzu haka?
Sheik El-Zakzaky: Ina samun sauki jami'an tsaro sun bari na gana da likitan. Ina godiya ga Allah. Ina samun sauki.
'Yan jarida: Kana da wani abu da za ka kara cewa.
Sheikh El-Zakzaky: Ina godiya ga addu'o'inku.
'Yan jarida: Mun gode
Sheikh El-Zakzaky: Na gode.

No comments:

Post a Comment