Thursday, 18 January 2018

Karo da tsuntsu ya tilastawa jirgin sama yin saukar gaggawa

Tsuntsun da ya yi karo da jirgi
Shugaban babban filin jirgin sama na Burundi ya tabbatar da cewa, wani jirgin sama dauke da sojoji ya daki wani tsuntsu bayan tashinsa a safiyar ranar Laraba.Matukin jirgin bai yi wata-wata ba ya juya zuwa baya domin komawa inda ya baro don a duba lafiyar jirgin a birnin Bujumbura.


Wakilin BBC ya ce Jirgin ya shafe kusan sa'a daya yana shawagi a wuri daya a sararin samaniya kafin ya sauka.
Babu dai wata matsalar na'ura da aka samu sakamakon karo da tsuntun. Daga baya dai jirgin ya sake tashi.
Jirgin dai ya debo sojoji ne inda zai kai su Somalia domin haduwa da dakarun Afirka da ke yaki da mayakan kungiyar al-Shabab.
Kasar Burundi dai na da dakaru masu yawa a cikin dakarun da ke yaki a Somalia.
bbchausa

No comments:

Post a Comment