Tuesday, 9 January 2018

Kasar China ta kammala ginin gada mafi tsawo a Duniya: Shekaru takwas akayi ana ginata

Wannan itace gadar kan ruwa data tafi kowace gadar kanruwa tsawo a Duniya, an ginatane a kasar China daga Hong Kong, Zhuhai zuwa Macao, tsawon gadar yakai  nisan kilomita hamsin da biyar.Shekaru shida akayi ana tsara da shirya yanda za'a gina gadar sannan kuma aka dauki shekaru takwas ana ginata, wani karin abin birgewa da mamaki dangane da wannan gada shine, ma'aikatan dake gininta sun gama ta a daidai ranar da aka kintaci cewa zasu gamata din babu kari babu ragi.
Ranat 31 ga watan Disambar shekarar 2017 aka tsara cewa za'a gama gina gadar kuma a ranar ma'aikatan suka kammala ginin ta babu kari babu ragi, wannan hoton na sama, wani tsibirine da injiniyoyi suka kirkira akan ruwa dan kayatar da gadar wanda a da babushi.
Duk wani babban aiki na gadar ya kare, sannan anyi gwajin wutar lantarki da zasu karawa gadar kyau da daukar ido, a wannan watan na Janairu da muke ciki ake sa ran za' a cigaba da gwada wasu sauran abubuwan gadar dan tabbatar da cewa tana aiki yanda ya kamata da kuma shareta-share da goge-goge kamin a fara hawanta. Daga cikin saukin tafiye-tafiyen da gadar zata kawo akwai rage nisan tafiya daga birnin Hong Kong zuwa birnin Zhuhai wanda awa ukune amma idan mutum zaibi takan gadar zaiyi mintuna talatinne kawai.

Xianhua.net

No comments:

Post a Comment