Sunday, 14 January 2018

Kasar China ta rushe wata katafariyar coci da aka gina akan hanya

Kasar China ta rushe wata coci da aka gina ba bisa ka'ida ba, cocin wadda mahukuntan kasar sukace an ginata akan filin da ya tare hanyar wucewar ababen hawa da kuma takurawa al'umma an saka nakiya aka mata rugu-rugu.Cocin babbace sosai domin tana daukar mutane akalla dubu hamsin sannan kuma an ginatane akan zunzurutun kudi dalar Amurka miliyan biyu da dubi dari shida, kamar yanda jaridar Independent ta kasar Ingila ta ruwaito.
Koda a shekarar 2009 rahotanni sun nuna cewa saida jami'an gwamnati sukazo cocin suka kwace baibul a hannun masu bauta sannan aka kama malaman cocin inda aka yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekaru bakwai.

No comments:

Post a Comment