Monday, 22 January 2018

Kash! Ta leko ta koma: Musulma ta farko me sanye da Hijabi da ta zama jakadiyar man gyaran gashi ta ajiye aikin: Wai dan ta taba cewa kasar Isra'ila haramtaciyar kasace a shekarar 2014

A jiyane mukaji labarin Amena Khan, Musulma, me son rufe gashin kanta daga kasar Ingila wadda ta zama Mace ta farko da ta taba yin tallar man gyaran gashi kanta a rufe da Hijabi a Duniya , anta yaba mata, mutane, harma da wadanda ba musulmai ba sunta yabon wannan sabon salo da aka fito dashi na karfafawa mata, musulmai masu saka Hijabi gwiwa, to saidai kamar yanda aka sani, dama a duk lokacin da tauraruwar mutum ta fara haskawa, aka sanshi a Duniya ta wani dalilli, to wasu suna nan suna neman hanyar da zasu dankwafar dashi.Wasu sunje sun zakulo wasu kalamai da Amina ta taba rubutawa akan dandalinta na sada zumunta tun shekarar 2014, lokacin yakin zirin Gaza, tsakani Falasdinawa da Yahudawan kasar Isra'ila, Amina, a wancan lokacin ta bayyana kasar Isra'ila a matsayin haramtacciyar kasa dake kashe kananan yara, haka kuma ta fasalta kasar da cewa kasar Fir'aunancice, saboda irin zalincin da sukewa Falasdinawa Duniya tana kallo.

Bayyanar wadannan kalamai yasa, yabon da akewa Amina a Duniya ya koma zargi da kuma kalaman batanci, musamman daga kasashen yamma, wanda dama kamfanin da ya bata jakadancin tallar man gashin daga can yake.

Dalilin haka kuwa yasa dole Amina ta goge wadancan kalamai da ta yi a twitter ta fito ta kuma baiwa Duniya hakuri inda tace "nayi matukar yin dana sanin abinda na rubuta akan kasar Isra'ila a dandalina na Twitter a shekarar 2014, kuma ina bayar da hakuri saboda irin batawa mutane rai da wadancan kalaman nawa sukayi, tace,"ina goyon bayan rarrabuwar al'umma daban-daban, bana nuna kyama ga kowa. Na goge kalaman dana rubuta saboda basu wakilci irin halayyar na'am da kowa da nake a kantaba, tace nashiga wata harkar talla(watau tallar man gashin kai) wanda naji dadin shiga ciki saboda irin yanda ta baiwa kowa dama(hadda musulmai masu Hijabi). Tace amma yanzu na yanke shawarar fita daga wannan tallar saboda irin labarai/surutan da akeyi akai sun canja daga na amincewa da kowa da kowa(zuwa na kiyayya)".

Me magana da yawun kamfanin L'Oreal wanda Amina ta fara yiwa tallar kayan gyaran gashin mata, ya bayyana cewa an gayamusu irin kalaman da Amina tayi a shekarar 2014 kuma sunji dadin irin yanda ta fito ta bayar da hakuri akan kalaman nata, haka kuma sun amince da janyewarta daga wannan tallar tasu. Ya kara da cewa kamfanin su yana maraba da kowa da kuma girmama kowane irin mutum, kamar yanda BBC ta ruwaito.

A gaskiya bamuji dadin wannan abuba kuma muna tare da Amina kuma muna mata fatan Allah ya bata wani abin mafiyin wannan kuma ya kara karfafa mata gwiwa fiye da da.

No comments:

Post a Comment