Sunday, 21 January 2018

Koda ban sake cin zabe ba: Duk wanda yazo baya zai gaji tsarin gwamnati me kyau">>Gwamna El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-rufai yayi wata magana data dauki hankulan mutane sosai a shafukan yanar gizo, gwamnan ya bayyana cewa "ko da ban samu an sake zabata a matsayin gwamnan jihar Kaduna ba, na gamsu da cewa duk wanda zaizo bayanmu zai gaji tsarin gwamnati me kyau da muka shirya, domin mun ajiye ginshiki me kyau na tafiyar da gwamnati a jihar Kaduna".


Wasu dai na sukar gwamnan jihar ta Kaduna akan wasu tsare-tsare da ya fito dasu a jihar, ciki hadda tsarin gyaran Ilimi indaya kori malamai dubu ashirin da biyu daga aiki bayan sun fadi wata jarabawa da yayi musu.  

No comments:

Post a Comment