Tuesday, 16 January 2018

KUNDIN TARIHI: Yadda Aka Kashe Marigayi Abubakar Tafawa Balewa(1966)

Kamar yadda tarihi ya nuna, mutumin da ya jagoranci bijirarrun sojojin da suka kashe manyan 'yan siyasar jamhuriy ta farko shi ne, Manjo Emmanuel Ifeajuna wanda dan Kabilar Igbo ne kuma tun yana dalibinsa a jami'ar Ibadan kafin ya shiga soja ya yi fice wajen tsageranci domin shi ne ya jagoranci tarzoman da daliban jami'ar suka y a 1956 na nuna adawa da ziyarar Sarauniyar Ingila.


A daren da suka shirya makarkashiyar kashe su Marigayi Tafawa Balewa, shi Manjo Emmanuel ya jagoranci bijirarrun sojojin su 22 wadanda kuma dukkanin su, 'yan Kabilar Igbo ne.  Bayan sun isa marabar Onikan, sai ya raba sojojin gida uku. Rukunin sojojin na farko a karkashin jagorancin Lt. G Ezedigo, an ba su umarnin cafko Ministan kudi na wancan lokacin, Cif Festus Okotie-Eboh.

Sai rukuni na biyu a karkashin jagorancin Onyeacham, su kuma ya ba su umarnin kula da motocinsu tare da tabbatar da cewa babu wata mota da za ta wuce ta marabar ba. Yayin da shi Manjo Emmanuel ya jagoranci sojojin da za su kai samame gidan Marigayi Tafawa Balewa kuma a bisa al'adarsa, ba kasafai Marigayi Tafawa Balewa ke amincewa a aje masa jami'an tsaro a gidansa ba ko in zai yi tafiya.

A shekarar 1964 ne, marigayin ya amince da Dogarin da aka nada masa a matsayinsa na Firayi Minista wanda zai kula da tsaron lafiyarsa mai suna Sajent Maxwell Orukpabo wanda shi ma, dan kabilar Igbo ne kuma a shekarar 1963 a lokacin wani taron majalisar rundunar 'yan sanda, Firimiyan Yankin Yarbawa, Akintola ya gabatar da bukatar a saya masu Motoci masu sulke saboda tsaron lafiyarsu amma Marigayi Tafawa Balewa ya jaddada masa cewa da ya amince da mallakar irin wannan motar don tafiye tafiye, gara ya yi murabus.

A kan haka ne, bijirarrun sojojin suka san ba za su fuskanci wata kalubale ba a yayin cafke Tafawa Balewa, don haka ne ma, sojojin da Manjo Emmanuel ya je da su gidan marigayin, ba wadanda aka horas da su ba ne don yaki. A lokacin da suka isa gidan marigayin, Manjo Emmanuel ya sa kafa ya haura kofar shiga gidan bayan da marigayin ya tambayi ko su wane ne a waje. Yana shiga cikin dakinsa, sai Manjo Emmanuel ya nunawa marigayin bindiga kuma ya ce sun zo ne don su cafke shi.

Sai Marigayi Tafawa Balewa ya nemi izininsu kan ya sanya tufafi inda ya saka farar jallabiyarsa ya kuma dauki Casbaha sannan suka tasa keyarsa gaba wanda a tsakanin mintina talatin sun cimma bukatarsu na cafke marigayin ba tare da harba ko da harsashi guda ba. A lokacin da suka iso inda suka aje motocinsu, wancan tawaga da aka ba umarnin cafko Ministan kudin, sun rigaya sun kamo shi a daure.

Sai suka tafi da su kuma bayan sun yi tafiya na wani dan gajeren lokaci sai Manjo Emmanuel ya bayar da umarnin a tsaya inda ya umarci Marigayi kan ya fito daga cikin motar, tamkar ya ba shi damar ya arce wanda kuma bayan marigayin ya fara sassarfa cikin jejin da ke kusa da hanyar sai Manjo Emmanuel ya dauko bindiga ya rika harbinsa har ya samu sa'a ya bindige shi har lahira wannan shi ne karshen rayuwar Marigayi Abubakar Tafawa Balewa a hannun wadannan 'yan kabilar Igbo. Allah Ya jikansa da RahamarSa.
Rariya

No comments:

Post a Comment