Thursday, 18 January 2018

Kungiyar malaman jihar Kaduna ta janye yajin aikin da take

Kungiyar malaman jihar Kaduna sun janye yajin aikin da suke dalilin korar da gwamnatin jihar tawa malamai dubu Ashirin da biyu a jihar, sanadin faduwa jarrabawa da aka gudanar. Gwamnan jihar ta Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya sanar da janye wannan yajin aikin yana cikin farin ciki.


Gwamnan ya kuma ce kungiyar malaman ta yabawa gwamnatinshi bisa irin tsare-tsarenta.

Gwamnan dai ya bayyana cewa yayi tsari na musamman dan koyar da malaman jihar dama sauran ma'aikata da auka ajiye aiki ayyukan dogaro dakai ya kuma yi musu tanadin bashi da zasu fara kasuwanci da harkokin noma.

No comments:

Post a Comment