Monday, 29 January 2018

Kyankyaso ya firgita wata mata tayi hadari da motarta

Kyankyaso ya tsorata wata mata 'yar shekaru sittin da daya a lokacin da take tukin mota ta firgice ta buga motarta da jikin gada, lamarin ya farune a kasar Singapore, matar tana cikin tuka motarta kirar Mazda kawai sai taga kyankyaso ya fito yana yawo nan da nan kuwa ta gigice sai kan motar ya kwacemata.Motar ta bugi karkashin wata gada kamar yanda ake iya gani a wannan hoton na sama kuma gaban motar ya lalace, matar dai bata ji wani mummunan ciwo ba, kuma danta yazo dan ya tafi da motar.
CNA/AA.

No comments:

Post a Comment