Friday, 26 January 2018

Majalisar dattijai ta baiwa NNPC wa'adin sati daya domin ya kawo karshen wahalar mai

Kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki ya bayyana cewa ya baiwa kamfanin mai na kasa, NNPC wa'adin sati daya domin ya kawo karshen matsalar wahalar man fetur da ake fama da ita a sassa faban-daban na kasarnan.Saraki ya kuma kara da cewa ya baiwa kwamitin majalisar dake kula da harkokin mai umarnin su hada rahoto nan da kwanaki bakwai su gabatar akan cewa ko kamfanin man na kasa yayi amfani da wannan umarni nasu.

Tun shekarar data gabatane a lokacin da bukukuwan Kirsimeti dana sabuwar shekara suka fara kunno kai ake ta fama da karancin mai a Najeriya kuma har yanzu matsalar taki ci taki cinyewa.

No comments:

Post a Comment