Thursday, 11 January 2018

Malamai masu zanga-zanga sun toshe kofar gidan gwamnatin jihar Kaduna duk da yawan jami'an tsaron da aka jibge

Malaman makaranta a jihar Kaduna sun fito zanga-zanga duk da dumbin jami'an tsaron da aka girke, a gurare daban- daban na birnin Kadunan. Tun daga titin Muhammadu Buhari Way motocin sojojine a girke sunata mazurai, haka ma a kofar gifan gwamnatin jihar an girke jami'an tsaro da dama, wasu rahotanni dai sun bayyana cewa gwamnatin jihar ta bayar da umarnin kama duk wani malamin daya fito yin zanga-zangar.Amma yanzu haka malaman suna can sun yi dandazo inda suka toshe kofar shiga gidan gwamnatin da kuma titin da yabi ta kofar gidan gwamnatun jihar, wannan yasa dole , duk da jami'an tsaron dake gurin.


Tun da safiyar yau, Alhamis aketa jin jiniyar jami'an tsaro suna ta zagaya cikin garin Kadunar.
Zuwa yanzu dai zanga-zangar na wakana cikin lumana babu wata alamartashin hankali.
A jikin kwalin da daya daga cikin masu zanga-zangar ya rike an rubuta cewa " Gwamna El-Rufai na bukatar amai gwajin tabin hankali".

No comments:

Post a Comment