Thursday, 11 January 2018

Mata ta gantsara wa mai fyade cizo a mazakuta

Wata mata mai ciki ta gantsara wa wani mutum da ya yi mata fyade cizo a kan mazakutarsa a kasar Afirka ta Kudu.


'Yan sanda sun ce mutumin ya yi wa matar fyade ne a kan idon danta bayan ya yi barazanar yanka ta da wuka lokacin da ya rage musu hanya a cikin motarsa a wani kauye da ke lardin Mpumalanga.

Mutumin ya yi wa matar, wadda cikinta ya kai wata uku, fyade ne bayan ya kai ta cikin daji sannan ya umarce ta da kada ta yi ihu, in ji 'yan sandan.

Sun kara da cewa "matar ta kokarta inda ta ciji mutumin a kan mazakutarsa ko da yake ya gudu bayan hakan".

Wata sanarwa da 'yan sandan suka fitar ta bukaci asibitoci su sanar da ita idan wani mutum da aka raunata a mazakuta ya kai kansa gare su domin su yi masa magani.

Matsalar fyade dai ta yi kamari a kasashen Afirka, inda ake kira a dauki matakan da suka dace wurin shawo kanta.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment