Tuesday, 23 January 2018

"Matasa sai kun shiga an dama daku idan kuna son shugabanci a kasarnan: Zage-zage a yanar gizo babu abinda zai canja">>Gwamna El-Rufai na Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya baiwa matasa wata muhimmiyar shawara akan shugabanci, da yawa matasan Najeriya sukan ce tun suna kanana ake fadin wata magana dake cewa sune shuwagabannin gobe amma har yanzu shuwagabannin da aka sani tun tale-tale sune da dangoginsu keta yin mulkin.Akan wannan batu Gwamna El-Rufai yace " Matasa suna tunanin cewa zagin shuwagabanni a kafofin yanar gizo na sada zumunta da muhawara zai iya canja yanda abubuwa ke faruwa a Najeriya. Babu wanda zai baku ragamar shugabanci kawai dan kuna matasa. Idan kana so ka zama shugaba to dole sai ka shiga an dama dakai, duk kuwa irin yanda kuke tunanin abin ya lalace/tabarbare. Ku wuni lafiya."
Tun bayan da gwamnan yayi wannan magana sai mutane, musamman matasan suka ta cewa wannan zance nashi haka yake kuma akata yaba mai.

No comments:

Post a Comment