Thursday, 18 January 2018

Me dokar bacci ya buge da gyangyadi

Wannan motar jami'an dake kula da ababen hawace na jihar Kaduna, wanda ake kira da KASTELEA a takaice, take dauke da kayan da suka wuce kima, kuma but din motar a bude, wani bawan Allahne ya dauki hoton inda ya jawo hankalin cewa da wanine ya dau irin wannan kaya a motarshi da sun kamashi., watau dai me dokar baccine ya buge da gyangyadi.


Mutumin ya rubuta cewa "Ka jarraba daukar irin wannan kaya a bayan motarka kaga yanda 'yan KASTELEA zasuyi caa a kanka kamar kuda yaga kashi, abin kunya dai ya kare akan masu kiran kamsu da hukuma amma suna taka doka, kuma ma motar ba'a yita dan daukar kayan nauyi irin wannan ba".

No comments:

Post a Comment