Thursday, 18 January 2018

Mun yi rantsuwa za mu yi gaskiya, saboda haka tsoron faduwa zabe, ba zai hana mu yin abin da muka tabbatar shi ne mafita ga al’umma ba. >>Gwamna El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufaiya bayyana cewa yasan wasu daga cikin tsare-tsarenshi na taba harkar siyasarshi, amma saboda tsoron faduwa zabe bazai hanashi tin abinda zai amfani al'umma ba.


A wani sako daya fitar ya bayyana cewa:

"Wasu daga cikin masu sukar mu suna mana barazana da faduwa zabe saboda irin tsauraran matakan da muke dauka don amfanin talakawa. Mun yi rantsuwa za mu yi gaskiya, saboda haka tsoron faduwa zabe, ba zai hana mu yin abin da muka tabbatar shi ne mafita ga al’umma ba. Muna sane cewa wasu manufofinmu suna da illa gare mu a siyasance amma muna da tabbacin cewa daukan wadannan matakan shi ne mafita ga al’umma. Muna da tabbacin cewa nan gaba al’ummar Jihar Kaduna za su zabi abin da zai amfane su da ‘ya’yansu."

No comments:

Post a Comment