Wednesday, 3 January 2018

"Na yiwa Umma Shehu tambaya akan addinine dan ta wake 'yan fim a gurin masu cemana jahilai">>Aminu Sharif Momo

A wata hira da tauraron fina-finan Hausa, Aminu Shariff, Momo yayi da bbchausa, ya wanke kanshi daga zargin da ake mai na cewa ya yiwa Umma Shehu tambayar addini dan ya tozartata a idon Duniya.Momo yace ya yiwa Ummar tambayarne dan ta wanke jaruman fina-finan Hausa daga gurin masu zaginsu da cewa basa karatu ko kuma basu da ilimin addini dana boko, kuma mutane basu fahimci Ummar bane amma bawai bata amsa tambayar da yaimata ba.

Ya kara da cewa kuma ya samu karfin gwiar yi mata tambayarne bayan data bayyana cewa bata cika damuwa da kallon fim ba saboda tana zuwa makaranta.

Gadai abinda Momon ya fadawa bbcn:


"Abin da ya sa na yi mata tambaya kan addini shi ne, na ga ana yawan yabawa 'yan fim maganganu cewa ba sa zuwa makaranta, ba su da ilimi musamman na addini ballantana na boko.

"Da na ji ta ce ba ta damu da kallon fim ba saboda tana zuwa makaranta sai na samu karsashin nunawa masu yi mana irin wancan kallo cewa 'bari na tambaye ta kan addini domin ta nuna musu cewa ba duka aka taru aka zama daya ba'.

"Kuma ina ganin fahimta ce mutane ba su yi ba shi ya sa suke ganin kamar ba ta amsa tambayar da na yi mata ba", in ji jarumin."

Haka kuma akan maganar cigaban masana'antar fina-finan na Hausa, Momo yace matukar suna son samun cigaba to sai sun daina yin fina-finai marasa Alkibla.

Akan wannan batu shima ga abinda ya bayyana:

"Babban kalubalen da muke fuskanta ita ce a samu manufa daya ko wata taswira da za a shata domin kai masana'antar Kannywood ga ci gabanta da kuma bunkasar harshen Hausa.
"Idan za a ci gaba da yin fina-finan da ba su da al-kibla, babu inda za a kai", in ji jarumin.

Aminu Sheriff, wanda ya ce babbar manufarsa ta soma fim ita ce a watsa harshe da al'adun Bahaushe a kasashen duniya, ya kara da cewa: "idan ba za mu iya yin hakan ba, babu riba a harkar Kannywood."

No comments:

Post a Comment