Thursday, 4 January 2018

Nan gaba Musulmai zasu fi yahudawa yawa a kasar Amurka saboda yawan haihuwa

About 3.45 million Muslims were living in the US in 2017, representing 1.1 percent of the population [Julie Jacobson/AP]
Rahotanni sun bayyana cewa yawan musulman kasar Amurka zai karu sosai nan da shekarar 2040 yanda zasu zamo addini na biyu mafi yawan mabiya bayan addinin kiristanci a kasar, a shekarar data gabatadai. 2017, anyi kiyasin cewa akwai musulmai miliyan uku dada dubu dari hudu da hamsin a kasar watau sama da kashi daya cikin dari na al'ummar kasar kenan.


Wani bincikene da masu bincike na Pew Research Center sukayi ya bayyana haka, kamar yanda Aljazeera ta ruwaito, binciken ya bayyana cewa a halin yanzu, Yahudawane ke gaban musulmi a yawa, bayan Kiristoci wanda sune sukafi kowane masu bin addini yawa a kasar ta Amurka.

Amma nan da zuwa shekarar 2050, musulmin zasu fi Yahudawa yawa a kasar, inda ake tsammani zasu karu zuwa mutane miliyan takwas da dubu dari daya, masu binciken sunce, tuna a binciken farko da sukayi a shekarar 2007, suka gano cewa yawan musulmin kasar ta Amurka na karuwa da mutane dubu dari duk shekara, wannan na faruwane dalilin yawan 'yan cirani dake shiga kasar da kuma yawan haihuwa da musulmin kasar keyi.

Addini Kiristanci dai shine akan gaba wajan yawan mabiya a kasar ta Amurka inda yake da kashi saba'in cikin dari na yawan al'ummar kasar.

No comments:

Post a Comment