Friday, 26 January 2018

'Obasanjo ya zama shugaban kamfen Buhari a shekarar 2019'

Me baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin majlisun tarayya, Sanata Ita Enang ya bayyana cewa maganganun da tsohon shugaban kasa, Obasanjo yayiwa shugaba Buhari a budaddiyar wasikar daya aikemai zasu taimakawa Buharin cin zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu.


Enang ya bayyana hakane a lokacin da yake ganawa da masu kula da harkokin watsa labaran na shugaba Buhari a yau, yace maganganun da Obasanjo yayi, ya fadi abinda ke damun da dama daga cikin 'yan Najeriyane kuma shi yana ganin cewa Obasanjon ba wai yace kada Buhari ya tsaya takarane ba, yana nufin cewa kamin ya tsaya takara yayi kokari ya magance matsalolin da ya zano.

Ya kara da cewa shi a ganinshi wannan dalilin ma yasa zai bayyana Obasanjon a matsayin shugaban Kamfe na Buhari a zabe me zuwa.

No comments:

Post a Comment