Sunday, 28 January 2018

"Obasanjo yayi gaskiya: Be kama Buhari ya kara tsayawa takara ba">>Sanata Shehu Sani

Sanata Shehu Sani me wakiltar Kaduna ta tsacikiya ya bayyana ra'ayinshi akan wasikar da tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya aikewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda ya shawarceshi da cewa kada ya tsaya takara a zaben shekarar 2019, Shehu Sanin yace Shima yana ganin cewa Buharin ya hakura ya koma gefe, ya kawo wani da yake ganin zai ci gaba da ayyukan daya fara.A wata hira da yayi da manema labarai, Sanata Shehu Sani yace duk masu zuwa fadar shugaban kasar suna cemai wai ya tsaya takara suna yine kawai saboda irin amfanin da zasu samu idan hakan ta kasance amma a bayan idon shugaban ba haka abin yake ba, saboda haka Shehu Sani yace ya kamata Shugaba Buhari ya mayar da hankali akan abinda ake fadi a bayan idonshi.

Akan Obasanjo kuwa, Shehu Sani cewa yayi, sunyi zaman gidan bursuna tare da Obasanjo kuma ya sanshi da gayawa mutane gaskiya, koda a wancan lokacin yakan gayawa ma'aikatan gidan bursunan gaskiya idan sukayi ba daidaiba.

A karshe yace shugaba Buhari yayi iya yinshi a mulkin Najeriya saboda haka ya idan zaben 2019 yazo kada ya tsaya takara, ya nemo wani daga cikin na kusa dashi da yake ganin zai ci gaba da ayyukan daya faro ya bashi, shi kuma ya koma gefe ya zama uban kasa.No comments:

Post a Comment