Wednesday, 17 January 2018

Ronaldinho yayi ritaya daga buga kwallo

Tauraron dan kwallon kafa, Ronaldinho, wanda ya matukar nishadantar da masoya kallon kwallon kafa yayi ritaya, duk da yake cewa tun shekarar 2015 ya bar buga kwallo amma sai yanzune yake bayyanawa a hukumance cewa ya rataye takalman nasa kamar yanda bbc ta ruwaito.


Dan shekaru talatin da bakwai, yana cikin 'yan wasan da suka ciyo wa kasarshi ta Brazil kofin Duniya a shekarar 2002, kuma yaci kofin zakarun turai a shekarar 2006 a kungiyarshi ta Barcelona, haka kuma yaci kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta Ballon d'or a shekarar 2005. Ronaldinhon ya kuma taba cin kyautar gwarzon dan kwallon kafar FIFA dadai sauran muhimman kyautuka da duk wani dan kwallo keda sha'awar samu.

Wani dan uwanshi me suna Roberto Assis ne ya bayyana ritayar tashi kuma yace zasu yi bikin kece raini dan murna.

No comments:

Post a Comment