Monday, 22 January 2018

Ronaldo ya ji rauni a Fuska

Kwararren dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya sami nasarar jefa kwallo bayan dogon lokaci a ranar Lahadi - amma ba cin kwallon da yayi ba ne ya ja hankalin 'yan kallo. Ya sami rauni a kansa, inda babu wata-wata ya ari wayar likitansa - domin ya duba raunin da ya samu a fuskarsa a "madubi".


Masu sharhi sun yi mamakin wannan halayyar ta Ronaldo, amma abin bai dame shi ba.
Wani mai sharhi na BBC ya ce, "Abin mamaki ba ya karewa, ga Ronaldo na duba fuskarsa a madubi tun kafin ya fita daga filin wasa."

Amma duka da zolayar da ya sha a shafukan sada zumunta, ciwon da ya samu a sanadiyyar duka da boot a kansa da Fabian Schar na Deportivo La Coruna yayi tsananin da aka cire shi daga wasan.

Duk da wannan batun ne ya danne yadda wasan yakasance - amma Ronaldo ya tabbatar da cewa har yanzu yan kan ganiyarsa - domin ya zura kwallo biyu kafin a cire shi.

Sakamakon karshe na wasan ya ba Real Madrid nasara da ci 7 da 1, lamarin da ya daga su zuwa mataki na hudu a gasar La Liga.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment