Friday, 12 January 2018

Sa'adiya Adam ta bada sara: Amina Soyayya da Shakuwa ta kira kalmar MALL da MALT: Itama ko kuskurene?

Wannan bidiyon na sama na dauke da tallar fim din Adam A. Zango na Gwaska da za'a nuna a Ado Bayero Mall dake Kano wanda jarumar fim din Haisar, Amina Soyayya da shakiwa tayi, to saidai wajan fadin kalmar MALL sai tace MALT.A shekarar data gabatane dai jarumar fina-finan Hausa, Sa'adiya Adam ta fara kiran MALL din da MALT itama a tallar wani fim da tayi, daga baya dai ta fito ta gyara kuskurenta sannan ta nemi a rika musu uzuri idan sunyi kuskure. To da alama ta samu magajiya.

No comments:

Post a Comment